BBC Hausa - 10155577962362608

BBC Hausa
BBC Hausa 36.4K Views
  • 1K
  • 1K
  • 200
Download MP4 SD 3.41MB
  • QR code for mobile device to download SD video

A ranar Talata ne aka yi jana'izar marigayi Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule, wanda ya rasu ranar Talata a kasar Masar sakamakon ciwon zuciya. Ya rasu yana da shekara 88 a duniya. Ya bar mata daya da 'ya'ya goma, 6 mata, 4 maza. Marigayi Dan masani ya yi ayyuka da dama. Ya yi malamin makaranta, ya yi aikin NA, ya shiga siyasa an zabe shi dan majalisa a 1959, ya zama ministan makamashi da man fetur da albarkatun kasa, ya zama jakadan Nigeria na dundundun a majalisar dinkin duniya. Ya taka rawa wajen samarwa kasashen Afirka da dama 'yanci. Shi ne ya bada shawarar kafa kungiyar tarayyar Afirka OAU/AU a wani taro da ya jagoranci wakilan Najeriya. Dubban mutanene suke halarci jana'izar ta Dan Masani wacce aka yi a fadar Sarkin Kano. An binne shi a makabartar Wali mai Geza a birnin Kano da yammacin Talata.

Posted 2 years ago in BUSINESS